Kwamitin sulhu na MDD ya kira taro mai taken “Karfafa huldar cude-ni-in-cude-ka, da yin kwaskwarima don kyautata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa” bisa shawarar kasar Sin, wato shugabar karba-karba ta kwamitin a wannan wata. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ne ya jagoranci taron wanda aka yi a jiya, yayin da babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya gabatar da rahoto kan batun. A sa’i daya kuma, wasu ministocin harkokin waje da wakilai na kasashe sama da 100 sun halarci wannan taro.
A yayin taron, Wang Yi ya bayyana cewa, akwai bukatar farfado da ainihin huldar cude-ni-in-cude-ka tsakanin kasashen duniya, tare da gaggauta gina tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa cikin adalci. Dangane da wannan batu, ya bayyana ra’ayoyi guda hudu na kasar Sin.
- Juyin-juya-halin Kyautata Muhalli: Rawar Da Kasar Sin Ke Takawa Wajen Samar Da Makoma Mai Kyau
- ASUU Reshen Jami’ar KASU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani
Da farko, ya ce, ya kamata a kare mulkin kai cikin adalci. A yayin da ake inganta tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa, ya kamata kasashen duniya su shiga aikin cikin adalci, da yanke shawara bisa adalci, da kuma cimma moriya cikin adalci.
Sa’an nan, ya kara da cewa, ya kamata a karfafa yanayin adalci a duniya. Bai kamata a mika harkokin kasashen duniya cikin hannayen wasu kasashe ba, domin kasashe masu tasowa suna da ikon gabatar da bukatunsu da kuma kare ikonsu.
Haka kuma, ya ce, ya kamata a yi hadin gwiwa yadda ya kamata.
A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan.
Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci.
Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)