Babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kamata ya yi Amurka ta dauki kwararan matakai don dawo da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka kan hanyar da ta dace.
Wang, daraktan ofishin hukumar kula da harkokin wajen na kwamitin kolin JKS ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, yayin ganawarsa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar ASEAN. Yana mai cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya ta hanyar zurfafa tattaunawa ta gaskiya, yayin ziyarar da Blinken ya kawo kasar Sin a watan da ya gabata.
Ya kara da cewa, muhimmiyar yarjejeniya ita ce komawa kan ajandar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, da daukar muhimmin mataki na tsara tsarin da ya dace wajen inganta alakar manyan kasashen biyu
Wang ya yi karin haske kan matsayar kasar Sin game da batun yankin Taiwan, inda ya bukaci Amurka da ta guji tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ba gaira ba dalili, ko kuma yin zagon kasa ga ikon mulkinta da ma cikakkun yankunanta, da dakatar da dakile ci gabanta ta fuskar tattalin arziki, da cinikayya, da harkokin kimiyya da fasaha, da mayar da kasar Sin saniyar ware, kana ta cire dukkan takunkumai na babu gaira babu dalili da ta kakkaba mata.
Game da wannan ganawa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau cewa, Wang Yi ya bayyana matsayin Sin kan tsaron yanar gizo da yaki da miyagun kwayoyi a yayin ganawar.
Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin tana tinkarar hare-hare ta yanar gizo da ake kai wa hukumominta a kowace rana, kuma yawancinsu daga Amurka. Ya ce Sin kasa ce da ta fi fama da hare-hare ta yanar gizo, don haka, bai kamata Amurka ta zarge ta kan wannan batu ba.
Ban da wannan kuma, Wang ya ce, Sin da Amurka sun yi tattaunawa kan batun maganin Fentanyl a yayin ganawar, inda Sin ta bayyana matsayinta da damuwarta. Wang Yi ya yi nuni da cewa, Sin ta fi tsayawa tsayin daka kan manufar yaki da miyagun kwayoyi a duniya, amma Amurka ba ta amince da kokarin Sin a wannan fanni ba, tana zargin Sin da amfani da irin maganin, da kuma kama mutanen Sin ba bisa doka ba. Ya ce ya kamata Amurka ta daidaita batun bisa yanayin na adalci da girmamawa da hadin gwiwa, da soke takunkumin da ta sakawa hukumomin Sin masu kula da ayyukan yaki da miyagun kwayoyi cikin hanzari, don kawar da cikas ga shawarwari da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim Yaya, Zainab)