ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Gana Da Manyan Jami’an Saudiyya Da Iran

by CGTN Hausa
3 years ago
Wang yi

Mambar ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Wang Yi, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Waleed Elkhereiji, da mataimakin ministan harkokin waje mai lura da harkokin siyasa na kasar Iran Ali Bagheri Kani, jiya Jumma’a a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. 

Manyan bakin sun iso kasar Sin ne domin gudanar da taron farko, na kwamitin hadin kan kasashen Sin da Saudiyya da Iran.

  • Sin Ta Yi Kira Da A Aiwatar Da Cikakken Kudurin Tsagaita Bude Wuta A Zirin Gaza 
  • Ya Kamata A Aiwatar Da Kudurin Kwamitin Sulhun MDD Kan Hana Bazuwar Makamai Kanana

Cikin jawabinsa yayin taron, mista Wang, wanda kuma shi ne daraktan hukumar lura da harkokin waje, ta kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya ce har kullum kasar Sin na goyon bayan al’ummun yankin Gabas ta Tsakiya, a kokarinsu na lalubo hanyar samar da ci gaba mai zaman kanta. Kaza lika, tana goyon bayan kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, game da burinsu na yin aiki tare, don warware matsalolin tsaro dake addabar yankinsu, kana tana goyon bayan Saudiyya da Iran, game da kokarinsu na ci gaba da ingiza matakan bunkasa dangantaka.

ADVERTISEMENT

Wang ya kara da cewa, Sin ta sha alwashin amfani da wannan taro wajen ingiza kawance na makwaftaka tsakanin Saudiyya da Iran, tare da ba da sabbin gudummawa ga bunkasa zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya.

Yayin taron sassan 3, manyan jami’an Saudiyya da Iran, sun bayyana burinsu na mara baya ga aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar Beijing. Yayin da ita kuma Sin ta jaddada aniyarta, ta taka muhimmiyar rawa, da goyon bayan Saudiyya da Iran, wajen ci gaba da aiwatar da matakan karfafa dangantaka. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Wang yi
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Abinci

‘Yan Bindiga Sun Yi Sanadin Tashin Farashin Kayan Abinci A Taraba

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.