Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York.
Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya ce kasar Sin tana son hada hannu da kasashen Afirka wajen kafa tsarin daidaita harkokin duniya mai adalci da kuma samar da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duniya. Wang Yi ya ce Sin tana yabawa kasar Uganda bisa muhimmiyar rawar da ta taka yayin da take shugabantar kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu wato NAM, da taya ta murnar zama kasar da ta hada kan kasashen BRICS, haka kuma, Sin tana son yin kokari tare da kasar Uganda wajen sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da tabbatar da adalci a duniya baki daya.
A nasa bangare, minista Odongo ya amince da tunanin girmama juna da tabbatar da ikon mallakar kasa da zaman daidaito da kuma adalci da kasar Sin da sauran kasashen BRICS suke bi, yana mai cewa kasarsa tana son yin kokari tare da kasashen BRICS da shiga bangare mai dacewa a duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp