• English
  • Business News
Sunday, July 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jiya Talata, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da sabon jakadan kasar Amurka dake kasar Sin David Perdue.

Da farko, Wang Yi ya yi maraba da zuwan Perdue kasar Sin, ya kuma yi fatan cewa, zai zama mai karfafa mu’amala a tsakanin Sin da Amurka, da taimakawa wajen warware sabani tsakanin Sin da Amurka, da kuma ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu gaba, domin ba da gudummawa wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka kamar yadda ake fatan gani.

  • Gwamnan Katsina Ya Bukaci Hadin Gwiwa Da ‘Yan Kasuwa Domin Cigaban Jihar
  • Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3% 

Wang Yi ya ce, nuna adalci da girmamawa shi ne tushen sada zumunci a tsakanin bangarorin biyu, kana, yin mu’amala da hadin gwiwa su ne hanyoyi kadai da za su amfani kowa da kowa.

Haka kuma, Wang Yi ya jaddada cewa, bayan tattaunawar da Sin da Amurka suka yi kan batutuwan raya tattalin arziki da cinikayya a birnin Geneva, kasar Sin ta aiwatar da ra’ayin daya da aka cimma yadda ya kamata. Amma, abin da ya bakanta ran kasar Sin shi ne, kwanan baya, kasar Amurka ta fitar da jerin matakai wadanda suka illata moriyar Sin, kuma Sin ta nuna adawa da hakan.

Kazalika, ya kamata kasar Amurka ta hada kai da Sin, yayin aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a watan Janairu na bana, domin samar da damammaki na kyautata dangantakar dake tsakanin sassan biyu.

Labarai Masu Nasaba

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba

A nasa bangare kuma, David Perdue ya ce, shugaba Donald Trump yana matukar girmama shugaba Xi Jinping, kuma yana da muhimmanci a ci gaba da karfafa mu’amala dake tsakanin shugabannin biyu. A matsayin jakadan kasar Amurka a kasar Sin, yana fatan yin mu’amala da bangaren Sin yadda ya kamata, bisa ka’idar girmama juna, da sauraron ra’ayoyin juna. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mutum 7 Sun Rasu Sakamakon Kifewar Kwale-kwale A Sakkwato 

Next Post

‘Yansanda Sun Kama Mutane 2 Da Makamai Masu Yawa A Jihar Nasarawa

Related

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

11 hours ago
Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba

12 hours ago
Xia Xueying: Muna Sayo Kashi 90% Na Kayan Aikinmu Daga Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Xia Xueying: Muna Sayo Kashi 90% Na Kayan Aikinmu Daga Kasar Sin

13 hours ago
Wakilin Sin: Hukumar Shiga Tsakani Ta Duniya Za Ta Karfafa Warware Takaddamar Kasa Da Kasa Cikin Lumana
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin: Hukumar Shiga Tsakani Ta Duniya Za Ta Karfafa Warware Takaddamar Kasa Da Kasa Cikin Lumana

14 hours ago
Xi Da Takwaransa Na Mauritania Ghazouani Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 60 Da Kulla Huldar Diflomasiyya
Daga Birnin Sin

Xi Da Takwaransa Na Mauritania Ghazouani Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 60 Da Kulla Huldar Diflomasiyya

15 hours ago
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

1 day ago
Next Post
‘Yansanda Sun Kama Mutane 2 Da Makamai Masu Yawa A Jihar Nasarawa

‘Yansanda Sun Kama Mutane 2 Da Makamai Masu Yawa A Jihar Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

July 20, 2025
Amfanin Kabewa A Jikin Mace

Amfanin Kabewa A Jikin Mace

July 20, 2025
Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

July 20, 2025
Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

July 19, 2025
An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

July 19, 2025
Yadda Donal Trump Ya Lashe Zaben Shugabancin Amurka

Putin Ya Fita Daga Raina – Trump

July 19, 2025
Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba

Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba

July 19, 2025
Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN

Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN

July 19, 2025
Xia Xueying: Muna Sayo Kashi 90% Na Kayan Aikinmu Daga Kasar Sin

Xia Xueying: Muna Sayo Kashi 90% Na Kayan Aikinmu Daga Kasar Sin

July 19, 2025
Lamine Yamal Na Fuskantar Bincike Kan Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa A Spain

Lamine Yamal Na Fuskantar Bincike Kan Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa A Spain

July 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.