Manyan jami’an kasashen Sin da na Amurka sun gudanar da zagayen tattaunawa daban-daban a Malta a ranakun Asabar da Lahadi, inda suka amince da ci gaba da yin musaya da tattaunawa mai zurfi, kan batutuwan da suka shafi Asiya da tekun Pasific, da harkokin teku, da kuma manufofin kasashen waje.
Taron ya gudana ne tsakanin darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi, da mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan.
Yayin ganawar Wang ya jaddada cewa, batun yankin Taiwan, shi ne jan layi na farko da bai kamata a ketare a alakar Sin da Amurka ba. Haka kuma waijibi ne Amurka ta martaba sanarwoyi uku da sassan biyu suka cimma a tsakaninsu, da girmama alkawarinta na kin tallafawa neman “‘yancin kai na Taiwan.” Bangarorin biyu sun gudanar da sahihiyar tattaunawa, mai ma’ana kan daidaita da ma inganta dangantakar kasashen biyu.
Wang ya ce, ci gaban kasar Sin yana da karfi, kuma yana bin dabaru na tarihi da ba makawa, ba za a iya dakatar da shi ba. Ya kara da cewa, ba za a iya tauye hakkin samun bunkasuwar al’ummar Sinawa ba.
Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da aiwatar da muhimman matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a birnin Balin kasar Indonesiya, da yin mu’amala da shawarwari masu zurfi tsakanin kasashen biyu kan harkokin Asiya da tekun Pasific, da harkokin teku da kuma manufofin kasashen waje. (Ibrahim)