Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya aike da sakon jaje ga takwaransa na kasar Pakistan Bilawal Bhutto, kan ambaliyar ruwa da ta afku a kasarsa.
Wang Yi ya bayyana cewa, ya kadu matuka da samun labarin cewa, wurare da dama a Pakistan sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi.
Ya ce, yana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma jajantawa wadanda suka jikkata, da mutanen yankin da lamarin ya shafa.
Ya kara da cewa, gwamnati da jama’ar kasar Sin, za su ci gaba da kasancewa tare da gwamnati da jama’ar Pakistan.
Kuma ya yi imanin cewa, karkashin jagorancin gwamnatin Pakistan, al’ummar kasar za su iya shawo kan bala’in. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp