Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce yana farin cikin ganin yadda manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama, ta bunkasa daga shawara zuwa manufar da aka cimma matsaya a kan ta, kana ta ci gaba dagawa daga tunani zuwa manufar zahiri, inda take ingiza sabbin sauye-sauye a duniyar yau.
Wang, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, lokacin da ake kaddamar da cibiyar nazari game da manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama a birnin Beijing.
- Harry Maguire Ya Sanya Hannun Kwantaragin Shekara Ɗaya A Manchester United
- Yawan Kudin Da Sin Ta Zuba Kan Layin Dogo Ya Kai Dala Biliyan 117 a 2024
Ya ce wannan manufa ita ce amsar da kasar Sin ta samar, game da irin duniyar da bil adama ke fatan samarwa, da yadda za a samar da ita, kuma manufar da ke kunshe da ka’idojin nasararta a zayyane, da tarin alfanu ga lokuta mabanbanta, kana mai matukar tasiri dake karade daukacin sassan kasa da kasa.
Wang Yi ya kara da cewa, “A halin da ake ciki, tarin kasashe da yankunan duniya na ci gaba da aiki tare da kasar Sin, wajen cimma nasarar gina al’umma mai makomar bai daya ta fannoni da dama. An kuma rubuta wannan manufa cikin kudurori masu yawa na babban taron MDD, da wasu bayanai masu nasaba da burin ingiza cudanyar sassan duniya daban daban”. (Saminu Alhassan)