Majalisar Dattawa ta ce kar ‘yan Nijeriya su tsammaci amincewa da naira tiriliyan 49.7 na harsashen kasafin kudin 2025 kafin ranar 31 ga watan Janairu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da naira biliyan 49.7 ga hadakar majalisar wakilai da na dattawa a ranar 18 ga watan Disamban 2024, tare da rokon ‘yan majalisan da su nazarci kasafin tare da amincewa da shi domin samun damar gudanar da ayyukan raya kasa a wannan sabuwar shekarar.
- Kudirin Dokar Haramta Amfani Da Kudaden Waje Ya Tsallake Karatu Na Farko A Majalisa
- Kwamitin Kasa Na Majalisar CPPCC Ta Kasar Sin Ya Yi Bikin Maraba Da Sabuwar Shekara
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja, ya ce kare kasafin ma’aikatu, rassa da sashi-sashi zai fara gudana a ranar 7 ga watan Janairun 2025.
Mai magana da yawun majalisar ya ce hadakar kwamitocin majalisar wakilai da na dattawa kan kasafin kudin za su gabatar da rahoton karshe kan aikinsu a kan kasafin a ranar 31 ga watan Janairu.
Kudirin kasafin kudin wanda tuni ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar wakilai da na dattawa.
Sanata Adaramodu ya tabbatar da cewa, “Hadakar kwamitocin majalisar dattawa da na wakilai za su fara ganawa da ma’aikatu, sashi-sashi da rassa a ranar 7 ga watan Janairu, kuma za a gabatar da rahoton karshe a ranar 31 ga watan Janairu.”