Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya ce ya kamata Sin da Amurka su lalubo hanya mafi dacewa ta jituwa a tsakaninsu a sabon zamani.
Wang Yi, wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne yayin zantawa ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, a jiya Jumma’a.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Gudanar Da Liyafar Sabuwar Shekara
- Yadda Rashin Kula Da Gyambo Ke Cinye Kashi
A cewarsa, shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump, sun riga sun tsara alkiblar raya dangantakar kasashen biyu. Yana cewa, ya kamata dukkan bangarorin su bi muhimmiyar matsayar da shugabannin biyu suka cimma, da ci gaba da tuntubar juna da ajiye bambance-bambancen dake akwai a gefe da fadada hadin gwiwa bisa girmama juna da zaman lumana da moriyar juna da inganta ci gaban dangantakarsu cikin aminci da dorewa, tare da lalubo hanya mafi dacewa ta tafiya tare a sabon zamani.
Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin ba ta burin zarcewa ko maye gurbin wata kasa, amma dole ne ta kare halaltattun hakkokinta na ci gaba. Yana mai nanata cewa, kasarsa ba za ta bari yankin Taiwan ya balle daga babban yankin kasar ba.
Bugu da kari, ya ce kamata ya yi manyan kasashe su rika gabatar da kansu a matsayin manya, inda ya yi fatan Marco Rubio zai nuna sanin ya kamata da taka muhimmiyar rawa ga makomar al’ummar Sin da Amurka da ma zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya. (Fa’iza Mustapha)