A yau ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da hadaddiyar tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na musulmi wadda ta hada da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud da mataimakin firaministan Jordan, kuma ministan harkokin wajen kasar Ayman Safadi da takwaransa na Masar Sameh Shoukry da kuma ministar harkokin wajen kasar Indonesia madam Retno Marsudi. Sauran sun hada da ministan harkokin wajen Palasdinu Riyad al-Maliki da sakatare janar na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa (OIC) Hussein Ibrahim Taha.
Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye tabbatar da moriyar kasashen Labarawa da na Musulmi, da nuna goyon baya ga Palasdinawa da su samu hakkinsu bisa doka. Ya ce Sin tana goyon bayan kasashen Larabawa da na Musulmi da su yi kokari kan wannan batu ta hanyar diplomasiyya. Kana Wang Yi ya bayar da ra’ayin Sin kan daidaita rikicin zirin Gaza da batun Palesdinu, wato a aiwatar da kudurorin kwamitin sulhu na MDD da babban taron MDD, da tsagaita bude wuta nan da nan, da bin dokokin kasa da kasa, musamman dokokin jin kai na duniya.
Wang Yi ya jaddada cewa, tilas ne a saurari ra’ayoyin Palasdinawa game da makomar Palasdinu, kana ya kamata a yi la’akari da damuwar kasashen dake yankin. A tsara duk hanyoyin daidaita batun bisa shirin daidaita matsaloli tsakanin Palesdinu da Isra’ila, da kuma tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankin. (Zainab)