Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagaranci ganawar da aka yi tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 14 ta kafar bidiyo a ranar 23 ga wata. Haka kuma ya jagoranci taron tattauna ci gaban kasa da kasa a jiya tare kuma da gabatar da wani muhimmin jawabi.
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi bayani kan manufofin da shugaba Xi ya gabatar, da tasiri mai zurfi da za su yi ga kasa da kasa.
Wang Yi ya bayyana cewa, ganawar da kasar Sin ta shirya tana da babbar ma’ana ga aikin tabbatar da adalci tsakanin kasa da kasa, da sake farfado da aikin raya kasa da kasa, da kuma ingiza aikin kafa kyakkyawar makomar bil Adama.
Ya ce a halin yanzu, ana ganin sabbin sauye-sauye a fadin duniya, don haka shugaba Xi ya gabatar da dabarun kasar Sin, da za su wanzar zaman lafiya da samun wadata a fadin duniya. Alal misali, tabbatar da adalci domin kwanciyar hankali a fadin duniya, da hada kai domin samun ci gaban kasa da kasa, da ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin samun ci gaba tare, da tafiya da zamani domin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, da kuma nacewa kan kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje domin ba da gudumowar kasar Sin kan farfadowar tattalin arzikin duniya. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)