Kwanan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasashen Vietnam, Malaysia da Cambodia bisa gayyatar da shugabannin kasashen uku suka yi masa. A karshen ziyararsa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin bayani kan ziyarar.
Wang Yi ya bayyana cewa, a yayin wannan ziyara, shugaba Xi Jinping ya halarci bukukuwa kusan 30, inda ya yi karin haske kan manufofin kasar Sin na zaman lumana tare da kasashe makwabta, da tabbatar wadatar kasashe makwabta, da kwanciyar hankali a yankunan da suke ciki, tare da sa kaimi ga cimma nasarar kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa fiye da dari daya, tsakanin kasar Sin da wadannan kasashen 3.
- Jerin Manyan Jaruman Fim Da Nijeriya Ta Rasa A Yan Shekarun Nan
- APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu – PDP Ta Zarge Su
Ban da haka, rahotannin da kafofin yada labaru na kasar Sin da na sauran kasashe suka watsa sun nuna cewa, wannan ziyara ta nuna yadda kasar Sin take son yin hadin gwiwa tare da kasashe makwabta wajen tinkarar dimbin kalubale daban daban, da nuna kyakkyawar niyyar kasar Sin ta kare ra’ayin damawa da bangarori da dama a duniya, da ka’idojin cinikayya na kasa da kasa. Kana ziyarar ta shugaba Xi na wannan karo, ta nuna yadda kasar Sin ke sauke nauyi bisa matsayinta na babbar kasa, yayin da duniyarmu ke fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da rudani.
A yayin wannan ziyara har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yakin cinikayya zai gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, da haifar da mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya, da tarnake halaltacciyar moriyar kasashen duniya, musamman ma ta kasashe masu tasowa.
Sai dai kuma, yayin da ake fuskantar karuwar masu nuna ra’ayin kariyar ciniki a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, kuma za ta ci gaba da samar da dimbin gudummawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya, in ji shugaban kasar Sin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp