A jiya Talata ne babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin Wang Yi ya yi kira ga kasashen BRICS da su kara yin hadin gwiwa a aikace wajen tinkarar kalubalen tsaro a duniya.
Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana daraktan ofishin kula da harkokin waje na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron masu ba da shawara kan harkokin tsaro na kasashen BRICS da wakilan manyan jami’an kasashen BRICS kan harkokin tsaro karo na 13 a Johannesburg, Afirka ta Kudu.
Wang ya ce BRICS dandali ne mai muhimmanci ga kasuwanni masu tasowa da kasashe masu tasowa don hada kai da karfafa kansu, Wang ya kara da cewa, hadin gwiwar BRICS ya samu sakamako mai ma’ana, da kuma bada kuzari ga duniya mai rauni.
Domin tinkarar kalubalen tsaro da duniya ke fuskanta a halin yanzu, da warware matsalolin tsaro, Wang ya bukaci kasashen BRICS da su kiyaye ka’idojin mutunta juna, da kiyaye manufofi da ka’idojin Yarjejeniya Ta Majalisar Dinkin Duniya, da mutunta martaban juna, da ‘yancin kasashe na zabin tsarin siyasarsu da hanyoyin ci gaba. (Yahaya)