Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen gabashin nahiyar Asiya da aka gudanar a Phnom Penh, hedkwatar kasar Gambodia, inda ya yi tir da sanarwar G7 game da batun yankin Taiwan na kasar Sin.
A cewar Wang Yi, sanarwar da G7 ta fitar ta mai da fari baki da jirkita gaskiya, kuma ta tsoma baki cikin matakai masu dacewa da Sin take dauka wajen kiyaye tsarin mulkinta da cikakken yankinta, Abin da ya fusata jama’ar Sinawa matuka. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp