A jiya ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da ‘yan jarida tare da ministan harkokin wajen kasar Solomon Islands Jeremiah Manele a birnin Honiara, inda ya yi bayani game da burin ziyararsa a yankin kudancin tekun Pasifik.
Wang Yi ya bayyana cewa, a shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugabannin kasashen tekun Pasifik, inda suka amince da inganta dangantakar dake tsakaninsu, zuwa matsayin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, tare da nuna girmamawa ga juna, da samun bunkasuwa tare, don haka, an bude sabon babi kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen tekun Pasifik.
A shekarun baya baya nan, an samu babban ci gaba, kan raya dangantakarsu, wanda hakan ya jawo babbar moriya ga jama’ar yankin, kana ya zama misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.
A kwanaki biyu da suka wuce, Sin ta gabatar da jerin ayyukan hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen tekun Pasifik, da kuma jerin ayyukan hadin gwiwar a tsakanin lardunan Guangdong, da Fujian, da Shandong na kasar Sin da kasashen tekun Pasifik, wannan ya shaida cewa, sada zumunta, da yin hadin gwiwa tare da kasashen tekun Pasifik sun riga sun zama muhimman ayyukan da hukumomin wuraren Sin suka gudanar.
Wang Yi ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da bin manufofi hudu kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen tekun Pasifik, wato nuna daidaito tsakanin su, da girmama juna, da yin hadin gwiwa don samun moriyar juna, da kuma kiyaye bude kofa ga kasashen waje, da amincewa da bambancin dake tsakaninsu. (Zainab)