Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, daga ranar 24 zuwa 25 ga wata, darektan ofishin hukumar kula da harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai halarci taron masu ba da shawara kan harkokin tsaro da wakilan manyan jami’an tsaron kasashen BRICS karo na 13 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, kana zai ziyarci kasashen Najeriya, da Kenya, da Afirka ta Kudu, da Turkiye kafin da kuma bayan taron.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning ta fitar, ta ce minista a fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu Khumbudzo Ntshavheni da gwamnatocin Najeriya da Kenya da Afirka ta Kudu da kuma Turkiye ne suka gayyaci Wang.
Haka kuma, dangane da kammala aikin gyaran magudanar tace ruwa ta zamani ta farko dake kasar Bangladesh kuwa, Mao Ning ta ce, wannan wani karin misali ne game da shawarar ziri daya da hanya daya da kasashe abokan hulda ke amfana da shi. Shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da guraben ayyukan yi dubu 420 ga kasashe abokan hulda tare da fitar da mutane kusan miliyan 40 daga kangin talauci a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Kasar Sin tana son yin aiki tare da kasashen duniya, don ci gaba da inganta aikin gina hadin gwiwa mai inganci game da shawarar “ziri daya da hanya daya” da taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya da samun ci gaba mai dorewa a duniya baki daya. (Mai fassara: Ibrahim)