Wani matashi dan shekara 32 mai suna Rayyanu ya rasu a cikin wani masallaci bayan sallar asuba a unguwar Paso dake karamar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin Paso mai suna Ibrahim Musa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 5:56 na safe lokacin da marigayi Rayyanu ya zo masallaci domin gudanar da Sallar Asuba.
- Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Na Kano Ya Yi Murabus Watanni 7 Bayan Naɗa Shi
- Kamfanin BYD Ya Samu Karin Ribar Kaso 34 Zuwa Dala Biliyan 5.6 A Bara
Ya ce marigayin ya zo masallacin ne da babur, sai ya yanke shawarar ya dan kwanta kadan bayan salla amma daga nan ya ce ga garinku nan.
Ya ce, “Da misalin karfe 7:28 na safe ne wasu da ke sharar masallacin suka ga mutumin a kwance a cikin masallacin, sai suka yi kokarin tayar da shi domin su yi shara amma shiru.
Nan da nan, sai mutanen suka sanar da Musulman yankin lamarin, inda suka garzaya da shi zuwa asibiti, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.
Musa ya ce, daga bisani aka mika gawar marigayin ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp