Connect with us

Nahiyar Afirka

Wani Limamin Coci Dan Kasar Italiya Ya Shiga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Nijar

Published

on

An yi garkuwa da wani limamin darikar Katolika dan asalin kasar Italiya a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar kusa da kan iyaka da Burkina Faso

Hukumomin Jamhuriyar da kuma kasar Italiya sun tabbatar jiya Talata cewa, an sace Pier Luigi Maccalli ranar Litinin da dare daga kauyen Bamoanga, dake tazarar kilomita dari da ishirin da biyar daga Niamey babban birnin kasar.

Nan da nan babu wanda ya dauki alhakin garkuwa da shi, wanda ya kasance mutum na biyu, dan kasashen yammaci da aka yi garkuwa dashi a kasar ta yammacin Afrika cikin wata guda.

Macalli ya shafe shekaru goma sha daya yana aiki a yankin tare da kungiyar ayyukan mishan ta Afrika, wata kungiyar aikin mishan ta darikar Katolika.

Kungiyoyin mayaka da suka hada da Boko Haram suna kara tada kayar baya a yankin da Nijar take iyaka da Mali da kuma Burkina Faso.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: