Wani Matashi wanda bai jima da kammala karatun digirinsa na farko a Jihar Neja ba, ya yi kokarin mayar da wasu makudan kudade da suka kusan Naira Miliyan 100 da a ka turo masa ta asusun ajiyarsa bisa kuskure.
Yanayin tura kudi zuwa ga wani asusun bisa kuskure, ba bakon abu ba ne a Nijeriya, to amma abin da yake yawan ba wa mutane mamaki shi ne yadda da yawa daga cikin wadanda suke tsintar kansu cikin wannan yanayin, suke mantawa da kuncin rayuwar da ake ciki, su bi tsarin addininsu ko al’adarsu wajen cigiya sabanin wadanda suke amfani da kudin ba tare da tsoron wanda ya halicce su ko kuma za a iya kama su ba.
Abubakar Muhammad, wanda yake taya mahaifinsa kasuwanci a Jihar Neja, ya shiga sahun irin wadannan mutanen na kirki, inda yana zaune kwatsam sai ya ji shigar kudi asusunsa na banki ba tare da sa rai ko kuma kulla ciniki kan kudin ba.
LEADERSHIP HAUSA ta zanta da Abubakar kan yanayin yadda al’amarin ya faru.
“Mun kulla huldar kasuwanci da wasu a kan za su turo mun da N310,000, kuma sun tura min kudin a ranar 19 ga watan Oktobar 2023.”
Abubakar ya ci gaba da bayyanawa LEADERSHIP HAUSA abinda ya faru a wannan ranar dai ta 19 ga watan Oktoban, in da ya ce, “Bayan kamar minti talatin da turo mun kudin da mukai ciniki a kansu, kawai sai na ga kuma wani sakon na nuna an sa mun Naira Miliyan 84,210,000, wanda kuma ni na san ba mu yi magnarsu ba.”
Abubakar wanda shekarunsa ba su haura Ashirin da Uku ba, ya yi mamaki mutuka da ganin irin wannan makudan kudade da suka kusan kaiwa miliyan 100 da suka shiga asusunsa.
“Ina zaune kawai sai na ga kira daga wadananan mutanen da muka yi cinikin da su, sai suka ce min sun yi kuskure kan kudin da suka turo mun, dan haka suna bukatar na maida musu.”
Ya zuwa yanzu damu ke hada wannan rahoton, Abubakar na magana da wadanda suka turo masa kudin dan ganin ya maida musu hakkinsu, kamar yadda muka tabbatar.
Wannan dai abun da Abubakar ya yi, ya nuna irin kishinsa ga addininsa, da kuma hakura da abunda ba nasa ba ne, halin da ya kamata matasa da al’umma su yi koyi da shi.