A karo na biyu ckin kasa da mako guda an sake samun wani babban mutum mai shekaru mai suna, Yakubu Mamza, da ya kashe kansa a Jihar Adamawa.
Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da wata mata mai suna, Florence Vandi, ta kashe kanta a Unguwar Viniklang da ke cikin Karamar Hukumar Girei ta Jihar Adamawa a sakamakon mutuwar saurayinta, lamarin da ya dagawa jama’a hankali, yanzu kuma ga wani mutum kuma a karo na biyu shi ma ya rataye kansa.
- Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Adamawa
- Al’ajabi: Saurayi Ya Yi Wa Zakara Fyade A Adamawa
Yakubu Mamza, wanda ke zaune a wani ginin da ba a kammala aikinsa ba a Unguwar rukunin gidaje 80 da ke Jimeta, ya kashe kansa a cikin gidan da yake kwana, ya rasu ya bar yaya da mata uku.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayi Yakubun, shekaru biyu kenan basa tare da matarsa, yana zaune shi kadai a cikin wannan ginin da ba a kammala aikinsa ba.
Kawo lokacin hada wannan rahoton ba a kai ga tantance dalilin da yasa ya rataye kansa ba, haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba game da mutuwar Yakubun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp