Wani mutum da aka bayyana sunansa da Osaro Owate, ya shiga hannun hukumar ‘yansandan jihar Ribas bisa zargin kashe mahaifiyarsa a kauyen Alesa da ke karamar hukumar Eleme kan rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu kan naira dubu goma (N10,000) kacal.
Wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa ya na fama da matsalar gaulanci ko tsatstsauran ra’ayin addini na tsawon sama da shekara 30, ya amsa da bakinsa kan cewa ya kashe mamar tasa da fartanya ne.
Da yake magana ta cikin wani faifayin bidiyon da ya yadu sosai a Soshal Midiya, Owate ya ce, ya bukaci naira dubu ashirin (N20,000) a wajen marigayiyar mamar tasa domin ya sayi kayan sawa da zan yi adon zuwa wajen bisne wata gawa, amma sai ta ba shi naira 10 kacal, kuma hakan ya kasa masa matuka
Wanda ake zargin ya ce, “Jiya (Ranar Juma’a), na fada mata zuwa safiyar Asabar ta ciro kudin da za ta bani da zan sanyi kayan sanyawa domin halartar bikin biso. Da safiyar yau din kafin na tashi sai ya zama ita ta kama shirye-shiryen fita daga gida domin ta je ta halarci bikin biso.
“Na tambayeta maganar kudin da na bukata daga wajenta na ce ko dai ba ta son na halarci wajen bison ne kuma. Sai ta ce to bari za ta ciro min kudin.
“Ta tafi ta je ta ciro N20,000 da muka hadu sai ta dauko N10,000 kacal ta ba ni. Na sha mamakin a inane zan samu kayan dubu goma na saya.
“Da na kama binta, sai ta fara musguna min da zagina wai sa’o’ina su na aiki su na sana’a don meye ni nake zaman banza bana sana’ar komai. Na tunatar da ita cewa ina fama da matsalar da ke damuna ta yaya zan je na nemi aiki alhalin ina da matsala.?
“Amma duk da hakan ta cigaba da surfamin fada kawai sai na bugeta da fartanya. Tana kicin domin dafa abinci ne lokacin da na buga mata fartanya. Da na fusata matuka, kawai sai na gama da ita. Idan ni ma rayuwata za ta kawo karshe don na yi hakan ba damuwa na mutun kawai na shirya ma hakan. Ina fama da matsalar gaulanci sama da shekara 30. Kamar yadda kuke kallona yanzu ina son na mutum.”
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton rundunar ‘yansandan jihar Ribas ba ta fitar da wani bayani a kai ba.