Wani mutum ya mutu bayan cinna wa kansa wuta a wajen kotun birnin New York inda ake shari’ar tsohon shugaban Amurka Donald Trump a ranar Juma’a.
A cewar NBC News, lamarin ya faru ne a wani yanki da aka kebe don zanga-zangar adawa ko goyon baya ga Trump.
- Sin Ta Nuna Rashin Gamsuwa Da Barazanar Da Amurka Ta Yi Na Kara Haraji Kan Karafa Da Gorar Ruwa Dake Shiga Kasar Daga Kasar Sin
- Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama
Marigayin, mai suna Maxwell Azzarello daga St. Augustine, Florida, yana tsakiyar shekaru 30 ne. A cewar ‘yansanda, kafin wannan aika-aika, an ga Azzarello yana watsa takardu dauke da rubutun da ya yi zargin makirce-makirce ce a cikinta. Daga nan sai ya zuba wa kansa barasa sannan ya kunna wa kansa wuta.
Shugaban masu bincike na Jami’an ‘yansanda bangaren NYPD, Joseph Kenny ya bayyana takardun da Azzarello ya watsa a matsayin “farfaganda, kusan rubutu ne kawai na makirci, mai ɗauke da bayanai game da shirin Ponzi da kuma iƙirarin cewa wasu cibiyoyin ilimi na cikin gida na gaba wajen rura wutar adawa.”
Jami’an NYPD hudu sun samu kananan raunuka yayin da suke kokarin ceto rayuwar Azzarello.
Azzarelo ya kona kansa ne jim kadan bayan kammala shari’ar Trump dangane da zargin kashe kudade.