‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a kauyen ‘Yan Kwada da ke cikin garin Farun Ruwa a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar, ciki har da masu shayarwa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a yankin a ranar Lahadi da yamma, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi sannan suka afka cikin gidaje da dama, sannan suka tafi da matan.
- Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno
- Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno
“Na samu labarin cewa, an sace mata biyar, wasu daga cikinsu, masu shayarwa ne a garin Farun Ruwa da ba ta da nisa da garinmu a safiyar yau (Litinin).
“‘Yan bindigar sun kai hari a sassan Shanono a yau, musamman a garuruwan da ke kan iyaka. Mutane da yawa suna shirin tserewa saboda tsoro,” in ji wani mazaunin Shanono, Ammar Wakili, wanda ya shaida wa wakilinmu.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kusan mako guda da ya gabata, rundunar tsaro ta hadin gwiwa sun yi bata kashi da wasu ‘yan bindiga a garin na Farun Ruwa wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe ‘yan bindigar da dama.













