• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
(250622) -- DAR ES SALAAM, June 22, 2025 (Xinhua) -- Zhang Junqiao (R) works in a surgery at Muhimbili National Hospital in Dar es Salaam, Tanzania, March 21, 2025. TO GO WITH "Feature: Chinese doctor remembered in Tanzania for heroic sacrifice" (Xinhua)

Kwanan baya, a asibitin Muhimbili National Hospital dake Dar es Salaam na Tanzania, mutane fiye da 300 sun halarci bikin zaman makokin wani likitan kasar Sin mai suna Zhang Junqiao. Zhang, wanda ya kasance shugaban tawagar likitocin Sin dake Tanzania lokacin rayuwarsa, ya rasu sakamakon kokarin ceton wata mace da ta fada cikin teku a Dar es Salaam, a ranar 15 ga wata. 

Zhang Junqiao ya taba fada cewa, “Zan yi kokarin zama wani nagartaccen likita duk tsawon rayuwata, don bauta wa jama’ar kasar Sin, da ta Tanzania, har ma ta duk duniya”. Wannan magana tasa ta nuna ruhin musamman na tawagogin jami’an lafiya na kasar Sin, na hakuri, da bauta wa jama’a, da kokarin ceton mutane, da nuna kishi da kauna ga kowa.

  • Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki A Janairun 2026 — Adedeji
  • Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara

Hakika tura tawagogin agajin aikin likitanci zuwa ketare wani muhimmin bangare ne na aikin kasar Sin na tallafa wa sauran kasashen da suke da bukata.

A shekarar 1963, kasar Sin ta tura tawagarta ta farko ta ba da agajin kiwon lafiya zuwa kasar Aljeriya. Daga baya, har zuwa shekarar 2023, a bisa kididdigar da aka yi a shekarar, kasar Sin ta tura likitoci dubu 30 zuwa kasashe da yankuna 76. Bayan da annobar Ebola ta barke a yammacin Afirka, kasar Sin ta tura likitoci fiye da 1200 zuwa wuraren da aka fi jin radadin annobar don ba da taimako. Kana a lokacin da ake samun bazuwar cutar COVID-19 a duniya, tawagogin likitocin Sin 46 dake kasashen Afirka daban daban, sun samar da gudummowa a kokarin dakile annobar a wuraren da suke. Sa’an nan, tawagogin likitocin Sin sun ba da kyautar dimbin magunguna da sauran kayayyakin aikin jinya ga wasu asibitocin kasashe masu tasowa, gami da taimaka musu horar da masu aikin likitanci.

Ko me ya sa kasar Sin ke son ba da taimako ga sauran kasashe a fannin aikin likitanci? Dalilin shi ne aikin ya dace da al’adun Sinawa na daukaka zaman lafiya da darajanta rayukan mutane. Wadannan al’adu sun sa kasar Sin son tabbatar da kwanciyar hankali maimakon ta da rikici, da kai dauki ga wadanda ke da bukata, maimakon nade hannu a yi kallo a gefe. Saboda haka, a lokacin da ake bukatar likitoci da magunguna a wasu kasashe masu tasowa, kasar Sin ta kan tura likitoci da samar da tallafi ba tare da jinkiri ba. Kana bayan da aka samu barkewar rikici a wasu kasashe, sojojin Sin su kan aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya a can, bisa izinin da Majalissar Dinkin Duniya (UN) ta ba su. Kana duk lokacin da wani iftila’i ya afku, kasar Sin ta kan tura tawagogin ceto, da aikewa da kayayyakin da ake bukata nan take, ba tare da wani jinkiri ba ko kadan.

LABARAI MASU NASABA

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke fuskanta, da tabbatar da kyakkyawar zamantakewa a duniya.

Wadannan tunani da imani na Sinawa ne suka kai marigayi Zhang Junqiao nahiyar Afirka, inda ya yi kokarin ba da taimako wajen ceton mutane, har ma ya sadaukar da ransa. Amma karin likitoci Sinawa suna ci gaba da kokarin nuna wannan imanin a wurare daban daban na duniyarmu. Da ka ga wadannan mutane, to, za ka yarda cewa, tabbas za a samar da duniya mai dadin zamantakewa da jituwa da ci gaba a wata rana. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?
Ra'ayi Riga

Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

October 23, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa
Ra'ayi Riga

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Next Post
An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” A Italiya

An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Sha'awar Xi Jinping Ga Al'adu” A Italiya

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.