Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin taya murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, inda ya takaita nasarorin da kasarsa ta cimma a shekarar 2024, gami da bayyana burinta a sabuwar shekara. A ganina, wannan jawabi ya karfafa zuciyar mutane daga wasu fannoni uku.
Na farko, yana karfafa zuciyarmu kan tattalin arzikin Sin.
- Rahoto: Sana’ar Watsa Labarai Ta Kasar Sin Ta Shiga Zamanin Cudanyar Digital Da Basira
- Takardun Kuɗi Sun Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 4.8 Duk Da Ƙarancin Kuɗi A Nijeriya
Ta la’akari da matsayin kasar Sin na babbar kawar kasashen Afirka a fannin hadin gwiwar tattalin arziki, babu shakka, yanayin ci gaban tattalin arzikin Sin yana haifar da babban tasiri kan nahiyar Afirka. To ko ta yaya tattalin arzikin kasar yake a shekarar 2024? Za a samu amsa cikin jawabin shugaba Xi, inda ya ce tattalin arzikin kasarsa ya samu farfadowa sosai: An yi hasashen cewa, GDPn kasar zai kai fiye da dalar Amurka tiriliyan 17.8, yayin da yawan hatsin da aka samar a kasar zai wuce ton miliyan 700, duk a shekarar ta 2024. Ban da haka, yunkurin wasu kasashen yamma na hana Sin samun ci gaba ta fuskar kimiyya da fasaha ya ci tura, ganin yadda kasar ta samu ci gaba sosai a fannin sabbin sana’o’i da masana’antu. A bara, yawan motoci masu amfani da wutar lantarki da aka samar a kasar Sin ya zarce miliyan 10 a karon farko, kana kasar ta samu dimbin sakamako a fannonin fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adam na AI, da na zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya, da dai makamantansu.
Na biyu, jawabin shugaba Xi ya sa mutane jin karfin zuci kan huldar dake tsakanin bangarorin Sin da Afirka.
Cikin jawabinsa, shugaban na kasar Sin ya ambaci yadda kasar ta karbi bakuncin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, da kokarin aiwatar da shirin raya “Ziri Daya da Hanya Daya”, duk a shekarar ta bara.
Hakika taron koli na FOCAC da ya gudana a birnin Beijing a wannan karo yana da ma’ana sosai. Saboda a wajen taron, an daga matsayin huldar dake tsakanin kasar Sin da dukkan kasashen Afirka da ta kulla huldar diplomasiyya da su, zuwa hulda mai muhimmanci da ta shafi manyan tsare-tsare, kana an sanar da dimbin shirye-shiryen ayyuka na zamanantar da Afirka, manya da kanana. A shekarar 2025 za a yi kokarin aiwatar da wadannan ayyukan da aka tsara.
Sa’an nan na uku shi ne, jawabin shugaba Xi ya ba mu kwarin gwiwa dangane da makomar kasashe masu tasowa, wato Global South.
Shugaba Xi ya ambata a cikin jawabinsa, kokarin da kasar Sin ta yi, wajen ingiza gyare-gyare a fannin gudanar da al’amuran duniya, da zurfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Kana ya gabatar da dabarar da za a iya bi, domin tinkarar kalubalolin da ake fuskantar a duniya, wato nuna hakuri da karamci don daidaita sabanin ra’ayi, da dora muhimmanci kan makomar dan Adam maimakon moriyar kai. Hakika, kasashe masu tasowa ne kadai ke iya daukar wannan dabara.
A shekarar 2024, yayin da wasu kasashen dake yammacin duniya ke neman katse huldar hadin kan kasa da kasa, da haifar da cikas ga tsarin dunkulewar kasuwannin duniya, mun shaida yadda aka habaka tsarin hadin gwiwa na BRICS, da yadda kungiyar kasashen Afirka ta AU ta halarci taron kolin G20 a matsayin mambar rukunin, da ma yadda aka shirya manyan tarukan kasa da kasa da dama a wasu kasashe masu tasowa, da suka hada da Peru da Brazil. Ban da haka, mun gane ma idanunmu yadda kasashen Afirka da kasar Sin suka zartas da ‘Sanarwar Beijing’, don bayyana kin yarda da ra’ayin nuna fin karfi, da yunkurin ta da rikici tsakanin rukunoni daban daban. Tabbas za mu ga yadda Sin da Afirka, tare da sauran kasashe masu tasowa, suka ci gaba da kokarin kare moriyar bai daya, da adalci, a shekarar 2025.
Kamar yadda shugaba Xi ya fada, ”Za a iya cimma duk wani buri, matukar ana kokarin nema.” Ina da imani kan cewar, hadin kan Sin da Afirka, da na dukkan kasashe masu tasowa baki daya, za su tabbatar da cikar burin kasar Sin da na kasashen Afirka, na samun zamanantarwa da ci gaban tattalin arziki. (Bello Wang)