Da nake karanta bayanan da aka rubuta a Facebook, na ga yawancin bayanai masu alaka da huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin sun nuna wani yanayi mai yakini da yabo. Sai dai ra’ayi riga, ba za a rasa wani mutum mai dauke da wani ra’ayi na daban ba. Misali, a ganin wasu mutane, wai “Sinawa sun yi kama da Turawa, sun je nahiyar Afirka don kwashe albarkatu maimakon raya wurin.” To, zan so in fada wa wadannan mutane cewa, idan ka samu damar karanta takardar bayanin da kasar Sin ta fitar a kwanan baya, wadda ta shafi tunanin kasar na raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, tabbas za ka samu wani ra’ayi na daban game da kasar ta Sin.
Sai dai mene ne “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”? Ma’anar ita ce, wani yanayin da ake ciki na samun hadin gwiwar mabambantan al’ummu da kasashe, inda suke tinkarar kalubaloli tare, da neman samun ci gaba na bai daya. Samun wannan yanayi shi ne babban burin kasar Sin ta fuskar hulda da sauran kasashe. Saboda haka, a lokacin da kasar Sin take ciniki da kasashen Afirka, da zuba jari a kasashen, da gaske ne tana neman samun cin moriya tare da kasashen Afirka, gami da ci gaba na bai daya. Yayin da matakan kwashe albarkatun wasu kasashe, da hana sauran kasashe ci gaba don neman kare matsayin wata kasa, suka saba da tushen tunanin Sinawa a fannin diplomasiyya.
- Tawagar Masu Aikin Na’urar Binciken Duniyar Wata Mai Suna Chang’e 5 Ta Kasar Sin Ta Samu Babbar Lambar Yabo
- Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana
To, mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ke ba da shawarar raya al’ummar dan Adam mai makomar bai daya? Dalili na farko shi ne, al’adun kasar na darajanta zaman lafiya, da neman samun daidaito tsakanin al’umma. Wannan al’adu ya zo daya da tunanin Ubuntu na Afirka, wanda ya jaddada muhimmancin dogaro da juna da hadin gwiwa a tsakanin mutane.
Sa’an nan wani dalili na daban shi ne yadda kasar Sin ta san ainihin abun da duniyarmu ke bukata, gami da makomarta a nan gaba. Duniyarmu tana fuskantar dimbin matsalolin da suka hada da koma bayan tattalin arziki, da gibin da ake samu a fannin raya kasa, da yake-yake, da lalacewar muhalli, da ta’addanci, da dai sauransu. Duk da haka, wasu kasashen dake yammacin duniya na ci gaba da yunkurin daukar matakan kashin dankali, da kulla kawance don jayayya da wasu, da yin babakere a duniya, wadanda tarihi ya riga ya shaida kuskurensu. To, me ya sa ake son maimaita kuskure? Abun da duniyarmu ke bukata, shi ne a daidaita matsalolin da ake fuskanta daga tushe, maimakon tura su zuwa sauran kasashe. Ganin haka ya sa kasar Sin ta gabatar da ra’ayin raya al’ummar dan Adam mai makomar bai daya, wanda ya daukaka hadin gwiwa, da cin moriya tare, gami da samun ci gaba na bai daya.
Tabbas, idan mun yi ihun cewa “Bari mu yi hadin gwiwa” kawai, maimakon daukar hakikanin mataki, to, ba zai yi amfani ba ko kadan. Amma sabanin haka, tunanin kasar Sin na raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya ya kunshi dimbin dabaru da manufofin da ake kokarin aiwatar da su. Inda dabarun suka hada da tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya, gami da daukaka ra’ayoyi na bude kofa ga ketare, da lura da moriyar kowa, da amfanawa juna, da samun daidaito, da wanzar da zaman lafiya yayin da ake kokarin raya kasa, da raya huldar kasa da kasa bisa daidaito, da adalci, da hadin kai, gami da daukaka ra’ayin samun bangarori masu fada a ji da yawa a duniya, da dai sauransu. Kana manufofin da ake aiwatar da su sun hada da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da matakan aiwatar da shawarwari na tabbatar da ci gaba, da tsaro, da raya wayewar kai a duniya, da dai makamantansu.
A karshe, ina so in ce, tunanin Sin na raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya yana da ma’anar musamman ga huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Saboda al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka irinta ce ta farko da aka gabatar a duniya. Kana halayen huldar dake tsakanin Sin da Afirka na nuna sahihanci, da zumunta, da zaman daidaiwa daida, da mai da adalci a gaban moriya, da kokarin biyan bukatun jama’a, da daukar hakikanan matakai masu amfani ba tare da bata lokaci ba, su ma sun tabbatar da matsayin hadin gwiwar Sin da Afirka na abin koyi a fannin raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. (Bello Wang)