Da yardar Ubangijinmu Allahu (SWT), wannan shi ne karshen batunmu game da al’amarin bashin da shugabanni irin su Gwamna da Shugaban Kasa ke ciwowa a cikin gida da ketare, wanda muka shafe Satika 14 muna fafata rubutu a kai.
Ba abin mamaki ba ne wani lokaci, wani dalili ya sanya mu kara cewa wani abu game da sabgar bashin, amma a wannan jikon, mun dangane da inda za mu ci burki, daga wannan rubutu namu na yanzu in shaa Allah.
A wannan gaba ta karkare rubutun namu, mai karatu ya kwana da sanin cewa, muna tattaunawa ne game da wasu shawarwarin da dabbaka su, zai matukar taimaka zuwa ga kauce wa tarkunan da Turawan Yamma ke dasa mana dare da rana, da sunan wai an ba mu bashin da zai farfado mana da tattalin arzikinmu, wanda ya jima da masassharar tunkuyar burji tsawon lokaci a wannan Kasa tamu ta Nijeriya da ba mu da tamkarta. Cikin abubuwa tara (9) da wannan marubuci ke kokarin gabatarwa a mahangar shawarwarin, ta tabbata cikin Makon da ya gabata, an gabatar da abubuwa ko a ce shawarwari uku (3) ne, saboda haka, yanzu a wannan rubutu, za mu tashi ne a shawara ta hudu (4) ke nan in shaa Allah.
Dakile Ta’adar Cin-hanci Da Rashawa A Kasa
Ba tare da dakile ta’ada ko halaiyar cin-hanci da rashawa ba, duk wani ingantaccen mataki na bunkasa tattalin arzikin Kasa da kowace gwamnati za ta dauka, a Nijeriya ne ko a wata Kasa a duk fadin Duniya, kwata-kwata ba za a kai ga gaci ba. Ko da kuwa za a sanya mamakon hannu jari a Kasar, kuma a shigar da basukan da aka ciwo cikin aiyukan da za su bunkasa, su hayaiyafa ta fuskar samun kudaden shiga “Productive Investments & Projects”, babu inda za a je, tattalin arzikin Kasar kuwa zai durkushe ne sannu a hankali, muddin za a daurewa sace kudaden al’uma gindi a Kasa. Da wuya cikin Duniyar yau, a samu wata Kasar da ake yin kwamacalar da ake yi a Nijeriya a cikinta, kuma a samu cewar har yanzu wannan Kasa na ci gaba da wanzuwa a ban-kasa.
Dole kodai a ga Kasar ta wargaje ne, kowa ya san inda dare yai masa, koko a wayigari ban da tafka mummunan yaki, babu abinda ake yi a Kasar, amma cikin ludufin Ubangiji, ban da Nijeriya, Kasar da ta hade duk wasu shika-shikai na tarwatsewa, amma cikin ikon Allah, har yanzu tana zaune daram, sai dai a hannun “yan sari ne take ta walagigi!
A Nijeriyar, ba abin mamaki ba ne idan aka ce, fadar shugaban Kasa, shi ne wani bigiren da ya fi ko’ina a Kasar daurewa cin-hanci da rashawa gindi! Tun da fadar na karkashin shugaban kasa ne, ke nan shi ne babban turun handama da babakere ke nan a duk fadin Kasar!. Da kuma mutum zai leka cikin kowace jiha a Kasar, zai samu cewa gidan gwamnatin jihar ne babban dandalin da ya fi kowane dandali cikin jihar daurewa wawure kudaden talakawan jihar gindi. Haka abin yake a matakin karamar hukuma, a nan kuma Ciyaman ne ake zargin zama babban Jugunu!.
Sai ka ji a Kasar an ce, ai tsohon shugaban Kasa wane, lokacin da yake mulki, ya umarci Babban Bankin Kasa, ya buga masa biliyoyin kudade dubbai nasa na kashin kansa ya totse.
Sai a ji cewa, wani shugaban, ya tattare kaso mai yawan gaske na dukiyar kasar, ya kai kasashen ketare ya jibge da sunan tasa ce. Wani shugaban kuma, sai a ce, lokacin da ya zo mika mulkin Kasar, ya je cikin lalitar Kasar da ke a Kasashen waje “foreign reserbe”, ya yi wa Kasar zigidir, ya lashe komai.
Wani shugaban kuma, sai ka ji an ce, ai biliyoyin dalolin Amurka ne ya ware da sunan zai bunkasa bangaren wutar lantarki na Kasar, amma shiru, Malam da Fasto sun ci ungulu, babu inganta lantarkin, kuma babu wadannan kudade a cikin lalitar gwamnati.
Wasu shugabannin kuwa, sai a samu cewa, na jikinsu, misali, abokanai, iyalai, “yan’uwa da sauran “yan korensu ne suka yi wa Kasar sintir! Sun lashe kudaden Kasar kaf! Bugu da kari, sun ciwowa Kasar basukan ketaren da sai an kere Shekaru dari (100) a na daruruwa a a ciki.
Babban abu mafi muni shi ne, irin wadancan tsofaffin shugabannin Kasar tamu ta Nijeriya, duk sata ko badakala ko wata almundahana da ake zarginsu da aikatawa, to fa, sun fi karfin tuhuma!. Labudda, idan dokar wannan Kasa ba ta da kaurin wuyar tuhumar tsoffin shugabannin Kasar da ake zargi da wani halin bera, to za mu jima ne ihunka banza cikin rijiya gaba dubu, game da bunkasar tattalin arzikinmu, ma’ana, arzikinmu zai ta durkushewa ne dare da rana.
A Nijeriyar jiya da yau, akwai wasu mutanen da za su iya biyawa Kasar bashin da ake binta a Ketare da kudaden al’uma da suka yi kwana da su, su zama mallakinsu, su da iyalansu. Amma ba za su yi ba, sun fi karfin doka, saboda su yaran tsohon shugaban Kasa wane ne. Ke nan, idan ba a fara tankado keyar tsoffin shugabannin wannan Kasa a na barin dokar kasa na yin hukunci a kansu ba, maganar inganta tattalin arzikin kasa a Kasar, zai zamto wani abu mai kama da tatsuniya ne illa-iyaka!.
Daukacin jihohin Nijeriya, cikin kowace jiha, akwai wasu tsirarun mutanen da idan an matsa su matsawa, daga cikin kayan al’umar Kasa da suka sata, za su iya biyawa jihar tasu basukan gida da na ketare da ta ciwo. Amma ina! Sun kasance shafaffu ne da mai, yaran tsohon shugaban Kasa wane ne!.
Suma gwamnoni ba a bar su a baya ba, wajen yin mummunar lahani ga tattalin arzikin jihohin nasu. Wai amma sai a wayigari ga gawurtaccen beran dimka cikin gwamnoni da aka kama dumu-dumu rungume da kayan sata, amma sai shugaban Kasa yai masa afuwa, a lokacin da za a iske barawon akuya ko agwagwa ya shafe wasu Shekaru a gidan gyaran hali (kurkuku), ba tare da sanin zuwa ma yaushe ne za a sallame shi?.
Duk Kasar da makaryata barayi ne “yan-lelenta, mafarki ne a yi tunanin tattalin arzikin wannan Kasa zai bunkasa! Yanzu haka cikin Duniya, daga Kasashen da muke burin kai wa ga matakin da suke kai na bunkasar tattalin arziki, wacce ce ta daurewa barayin Kasar gindin lakume asusun Kasar? Wace Kasa ce cikinsu, wadda take manyan barayin Kasar ne ababen girmamawa a idon jahilai da malamai tamkar irin yadda ake ciki a Nijeriya?
Dole ne a bi duk wata hanya mai yiwuwa wajen dakile ta’adar cin-hanci da rashawa, muddin a na son tattalin arzikin wannan Kasa tamu ya inganta. Dole ne Doka ta fi karfin kowa a Kasa, kowa da kowa duka abu guda ne a idon doka “rule of law”!!!.
Ba shugaban Kasa ko gwamna ne ba kawai ake yi wa zargin rub da ciki bisa lalitar Kasa, ko alama! Tun daga matakin Kasa zuwa jiha, zuwa karamar hukuma, akwai zargin yin almubazzaranci tare da cin dukiyar jama’ar Kasa ta haramtaccitar hanya. To dole ne a dode duk wata kafa da za ta bayu zuwa ga wannan mummunar ta’ada ta wawure dukiyar talakawa raunana a Kasa.
Rage Dawainiyar Tafiyar Da Gwamnati
Da daman mutane cikinsu har da tsohon shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, sun koka da irin yadda ake kashewa manyan majalisu biyu a Kasa biliyoyin kudaden jama’ar Kasa, da sunan tafiyar da su, batu ne ake na Majalisar Dattijai da ta Wakilai. Babu shakka wadannan tagwayen majalisu biyu na yin hafzi ne da biliyoyin kudade dare da rana, ba tare da share hawayen wadanda suka zabe su ba. Shi ya sanya jama’a da dama cikin Kasar na da tunanin kwalliya ba ta biyan kudin sabulu game da irin kwazon da ya kamata a ce wadannan majalisu sun nuna.
Sun gaza tankwara bangaren zartarwar Kasar, don gabatarwa da al’umar Kasa ingantacciyar rayuwa. Jama’ar Kasa kan sanya ayoyin tambaya akai akai game da shin, wace irin amfanuwa ne ma suke yi da gungun Majalisun biyu. Sau da daman lokuta, an ta gabatar da kididdiga iri-iri game da mamakon kudin da ake narkawa wadannan Majalisu biyu, sama da akasarin kasashen Duniya, cikinsu har da Amurka.
Su IBB da sauransu, na da ra’ayin a koma ne kacokan ga tsarin Majalisa guda maimakon biyu, duba da yanayi maras kyawo da tattalin arzikin wannan Kasa ke ciki. Babu shakka, da yawan mutane na da irin wannan ra’ayi.
Sannan, idan kuma ya zamana sai an zauna ne da Majalisun biyu, to lallai ne a sake fasalta irin makudan kudaden da majalisun ke hadiyewa daga kasafin kudi na kasa, ta yadda za a zaftare zaftarewa.
Uwa-uba fadar shugaban Kasa, lallai ne ita ma fadar shugaban Kasa, ministoci da sauran manyan jami’an gwamnatin taraiya su yi karatun ta-natsu, su gaggauta tsuke bakunan aljifansu, da sunan kudaden tafiyar da gwamnati. Biliyoyin kudaden alawus alawus, na tafiye tafiye da sauransu, duka dole ne a yi musu kwaskwarima, ta yadda za su yi kwabo da kwabo da halin tabarbarewar tattalin arzikin Kasar a yau.
Gwamnoni ma dole ne su yi taka-tsantsan, wajen yin bushasha da kudaden gwamnati, da sunan kudaden tafiyar da aiyukan gwamnati. Su dama kananan hukumomin Kasar, tuni gwamnoni suka yi musu dungulmin kudaden tafiyar da gwamnatocin nasu.
Samar Da Nagartaccen Shugabanci A Kasa
Kusan a ce, samar da nagartaccen shugabanci a Kasa, shi ne wani yunkuri mafi girma da jama’ar Kasa za su yi, don bunkasa rayuwarsu ta yau da kullum.
Mutane su kaucewa siyasar kudi, su rabu da gurbataccen tunani irin na jam’iyun siyasunmu na yau, su rika tsayawa tsai, tare da zabo wadanda suka cancanta, su mara musu baya, a matakin kasa da jiha da karamar hukuma har ma zuwa ga matakin mazaba. Rashin zabo mutane nagari, shi ne babban matakin annoba mafi girma wajen kassara al’umar Kasa da kuma tattalin arzikinsu!
Kirkirar Nagartattun Manufofin Tattalin Arzikin Kasa
Lallai ne gwamnatoci a mabanbantan matakai, su rika kirkirar nagartattun manufofin tafiyar da tattalin arzikin Kasa. Ya zamana manufofin, an tuntubi masana yayin kirkirarsu da kuma hanyar da za a bi wajen aiwatar da su. Ja da baya, ga wata manufa da gwamnati za ta yi, don kirkirar wadda ta fi ta, bai zama laifi ba. Daukacin manufofin, su zamto masu rinjayen amfanarwa ne kai-tsaye ga “yan Kasa sama da waninsu.
Aiwatar Da Kyawawan Manufofi A Aikace
Duk kyawon manufofin da za a samar, muddin ba a dabbaka su a aikace ba, to fa ba a ce komai ba. Saboda haka, duk wata nagartacciyar manufa ta tattalin arziki da gwamnati ta kirkira, sai a gaggauta dabbaka ta don bunkasar tattalin arzikin Kasa ba tare da yin wani jinkiri ba.
Dorawa Daga Inda Aka Tsaya
Duk wata gwamnati da ta maye gurbin wata, to wajibinta ne ta dora bisa wata kyakyawar manufar bunkasa tattalin arzikin Kasa da gwamnatin da ta shude ta samar, ba tare da nuna wata wariya ko banbancin siyasa ba. Da yawan kyawawan manufofin kyautata tattalin arzikin Kasa ba safai ne yake yin dogon zango ba musamman a Kasashen Afurka, kawai saboda banbancin ra’ayin siyasa!.
Akwai ma wasu shawarwarin jingim, wadanda ba a gabatar da su ba a wannan rubutu, amma kuma suna taka kyakkyawar rawa wajen bunkasar tattalin arzikin Kasa.
YANZU KALLO YA KOMA WAJEN GANIN IRIN MANUFOFIN TATTALIN ARZIKIN KASA DA GWAMNATIN AHMED BOLA TINUBU ZA TA ZO DA SU.
Mun Kammala!zs