Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanya hannu a hukumance kan kudurin da zai sa kaimi ga samar da shawarwari kan batun Xizang (wato Tibet) da Sin, a ranar 12 ga watan Yuli, wanda ya nuna cewa, gwamnatin Amurka ba ta taba daukar matsayin cewa Xizang yanki ne na kasar Sin ba tun a zamanin da, da cewa dole ne a warware sabani tsakanin Xizang da kasar Sin ta hanyar lumana bisa dokokin kasa da kasa ta hanyar tattaunawa ba tare da wani sharadi ba.
Wannan wasan karta fakewa ne da guzuma don a harbi karsana, da kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Yankin Xizang mai cin gashin kansa wani bangare ne na kasar Sin tun fil azal, kuma harkokin Xizang lamari ne na cikin gida na kasar Sin, wanda ba ya bukatar tsangwama daga wani bangare daga waje. Binciken kayan tarihi da aka yi a wannan yanki na kudu maso yammacin kasar Sin ya nuna dadadden alaka mai karfi da kusanci tsakaninsa da sauran yankunan kasar Sin, wanda ya tabbatar da hadin kan al’ummar kasar Sin mai mabambantan al’adu.
- Masana Sun Yi Kira Da A Fadada Musayar Al’adu Da Yawon Shakatawa Tsakanin Sin Da Najeriya
- Shugaban Kasar Sin Ya Jajantawa Donald Trump
Misali, daga cikin kayayyakin tarihi da aka gano a kabarin Guru Jiamu da ke Ali, a wannan yanki, wanda ya samo asali ne daga daular Han ta Gabas kimanin shekaru 2,000 da suka gabata, akwai wani kayan surfani da ya kwashe sama da shekaru 1,800 da suka gabata wanda aka tsara da zanen tsuntsaye da namomin jeji, yana dauke da harafin Sinanci “wanghou,” ma’ana girma, kuma shi ne kayan tarihi na siliki na farko da aka samu a kan tudun Qinghai-Xizang, wanda ya tabbatar da dogon tarihin mu’amalar kud-da-kud tsakanin yankin da sauran sassa da kabilun kasar.
Kokarin gurbata gaskiya ta hanyar kafa dokokin cikin gida kuma bisa radin kai da kuma musanta tarihin cewa Xizang wani bangare ne na kasar Sin tun a zamanin da, wata dabara ce mai cike da rudani don bata wa kasar Sin mutuncinta. Dole ne Amurka ta mutunta ka’idar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, ta kuma daina goyon bayan duk wani nau’i na neman “yancin kai na Xizang”, da kuma janye sabuwar dokarta ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Tabbas wannan yunkurin karkata gaskiya zai gaza, kuma zai fuskanci adawa ba da kasar Sin kawai ba, har ma da daga sauran kasashen duniya. (Mohammed Yahaya)