A yayin da aka bude wasannin lokacin sanyin na Asiya karo na 9 a birnin Harbin na arewacin kasar Sin a ranar Litinin ta hanyar gabatar da tseren kunna fitila, mai dauke da fitilar, kuma mamban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC), Yu Zaiqing, ya bayyana cewa, gasar za ta sa kaimi ga kara yawan wasannin lokacin sanyi a nahiyar Asiya.
Yu ya kara da cewa, tseren fitilar na dauke da ruhin Olympics, wanda ke sanya karin mutane samun zurfin fahimtar wasannin, yana mai cewa, wannan shi ne karo na biyu da Harbin ya karbi bakuncin wasannin lokacin sanyi na Asiya, bayan na karo na 3 da ya gudana a shekarar 1996. Ana matukar sa ran samun ingantattun wuraren gudanar da wasannin da ma mafi kyawun wasannin daga masu wasannin motsa jiki.
Wasannin lokacin sanyi na Asiya na Harbin na 2025 shi ne cikakkun wasannin motsa jiki na lokacin sanyi na kasa da kasa da aka gudanar a kasar Sin a baya-bayan nan, tun bayan gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022 ta Beijing. (Mai fassara : Mohammed Yahaya)