Matasa su ne makomar kasa. Tun da dadewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping yake nuna kulawar musamman game da ci gaban matasa, kuma sau da yawa yana tattaunawa da matasa ta hanyar wasiku.
A watan Yuni na shekarar 2003, Lin Dongmei, wata yarinya daga lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, ta samu wasika daga Xi Jinping, wanda shi ne daraktan kwamitin jam’iyyar JKS reshen lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, a lokacin.
A shekara ta 1994, ta hanyar aikin jin kai na “Project Hope”, Xi Jinping ya hadu da Lin Dongmei, yariniyar dake fama da talauci.
A cikin shekaru 12 da suka biyo baya, Xi Jinping ya yi amfani da wani bangare na albashinsa wajen tallafa mata a kowace shekara, tun tana aji hudu a makarantar firamare har ta kammala karatu a jami’a.
A cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, daga karatu zuwa aiki, daga karamar yarinya zuwa matashiya, Lin Dongmei ta samu jimillar wasiku biyar daga Xi Jinping.
Kalmomi gajeru ne amma suna da ma’ana, kuma sun jagoranci hanyar ci gaban Lin Dongmei. Yanzu, bayan da ta yi aiki na fiye da shekaru 10, Lin Dongmei tana kashe akalla albashin wata guda a kowace shekara wajen taimaka wa talakawa don samar musu da makoma mai haske.
Daga cikin abokan sa da su kan rubuta wasiku ga juna da Xi Jinping, akwai kuma matasan kasashen waje da dama.
A ranar 17 ga watan Mayu na shekarar 2020, Xi Jinping ya rubuta wasika ga dukkan daliban Pakistan dake karatu a jami’ar kimiyya da fasaha ta Beijing, inda ya yi maraba ga fitattun matasa daga kasashe daban daban don su yi karatu a kasar Sin.
Ya kara karfafa musu gwiwa da su kara yin mu’amala da matasan kasar Sin, da yin kokari tare da matasa daga ko’ina cikin duniya don ba da gudummawarsu wajen inganta cudanya tsakanin jama’a da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil-Adam.
Akwai wasiku da yawa da Xi Jinping ya rubuta ga matasa, wanda hakan ya zaburar da su, su yi aiki tukuru. (Mai fassara: Bilkisu Xin)