Rundunar ‘yansandan Jihar Imo, ta ce ta kama mutum tara da ake zargi ‘ya’yan kungiya IPOB a jihar.
An kama su ne, bisa zargin kashe ‘yansanda biyar da wasu fararen Hula biyu, dake a karamar hukumar Ngor-Okpala da ke a jihar.
- Sarkin Da Ya Fi Dadewa A Karagar Mulki Ya Rasu
- Sojoji Sun Kai Farmaki Masana’antar Kera Bindiga, Sun Yi Kame A Taraba
Kamen dai ya zo ne biyo bayan karytawar da kungiyar ta IPOB na cewa, wasu daga cikin ‘ya’yanta sun kashe ‘yansanda da wasu ma’aurata.
An cafko wadanda ake zargin ne, a wata maboyarsu da ke a Itu da ke a yankin Ezinihitte-Mbaise.
A cikin sanarar da kakakin rundunra jihar Henry Okoye ya fitar ya ce, an cafke su ne biyo bayan bin sahun su da tawagar jami’an tasro ta musamman na rundunr da SP Odeyeyiwa Oladimeji ya jagoranta, inda ya sanar da cewa, sun kama wani mai suna Mathew Chukwuma dan shekara 48 da ya fito daga yankin Mpam da ke a karamar hukumar Ahiazu-Mbaise Imo, a maboyarsa da ke a Umuahia a Jihar Abia.
Ya ce, bayan rundunar ta bincike shi ya amsa cewa shi dan kungiyar IPOB da ke a Mbaise, inda kuma ya taimakawa jami’an wajen kamo wasu abona ta’asarsa Ojoko Ikechukwu, dan shekara 53 da ya fito daga yankin Umugwa, sai wani mai suna Chilaka Charles dan shekara 44 da ya fito daga yankin Umuezuo sai kuma Anthony Iwu dan shekara 50 da ya fito daga yankin Umugwa da ya fito daga yankin Umuokirika da ke a karamar hukumar Ahiazu-Mbaise cikin jihar Imo.
Ya bayyana cewa, bayan rundunar ta bincke su, sun masa cewa su ‘ya’yan kungiyar IPOB da suka jima sun addabar alummar jihar Imo kuma da hanun su aka hallaka ‘yansandan biyar a kwanan baya da wasu fararen hula biyu a karamar hukumar Ngor-Okpala.
Acewarsa, wadanda kuma aka kama a Itu, akwai wani mai suna Damian Ibe dan shekara 50 sai Iwuala Simeon dan shekara 31 wadanda dukkanin su, sun fito ne daga yankin Mpam, da ke a karamar hukumar Ahiazu-Mbaise sai kuma wani Obali Paul dan shekara 70, da ya fito daga Itu a karamar hukumar Ezinihitte-Mbaise da ke a Imo.
Ya ce, Paul ya kasance dan malamin Coci ne wanda ya ke a cikin gungun masu aikta laifuka, inda ya bayyana cewa, sauran kuma sun arce, dauke da harbin Albarusai a jikinsu.
Wasu daga cikin makaman da aka samu a gunsu sun hada da, bindigar kirar AK47, Abarusai da bindun da ake kirawa a gida da sauransu.