A ranar 16 ga wata Yuni ne aka daura auren shahararrun masoyan TikTok Al’amin G Fresh wanda aka fi sani da Kano State Material tare da Amaryarsa Sadiya Haruna.
Auren da ya dauki hankulan mutane da dama musamman masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani da suka hada da Facebook da kuma TikTok din.
Sai dai jim kadan bayan tarewar Ango a gidan Amarya kuma sai ta tafi aikin Hajji a kasa mai tsarki wanda hakan ya sa G-Fresh kullum ya dinga yada bidiyon sa, yana sambatun shaudin rabuwa da amaryarsa.
A kwanakin baya ne dai aka dinga yada wata jita-jita cewar auren taurarin Tiktok din, Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen Kano state material ya mutu, sai dai daga baya ya fito ya bayyana cewa auren yana nan daram ba kamar yadda ake ta yayatawa ba.
Lauyar G Fresh Barr. Fatima Aliyu ta bayyana cewar har yanzu G Fresh na matukar kaunar matar sa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba kuma shima G-Fresh din yasha nanatawa a shafinsa na TikTok cewa yana son matarsa kuma ba zai iya rabuwa da ita ba.
Amma bayan dawowar amarya sai ga labari ya cika TikTok da sauran kafafen sada zumunta cewa wai auren taurarin biyu ya mutu inda har ma wasu ‘yan TikTok na cewa wai G-fresh ya yi yaji ne daga gidan Sayyada Sadiya ya koma kwanan shago bayan da aka samu sabani a tsakaninsu.
Wasu rahotanni sun ruwaito cewar tun farko Sayyada Sadiya ta mayar da shafinta na TikTok wurin tallata magunagunan gargajiya da take sayarwa kuma ta goge duk wani bidiyo da ta yi a baya ciki kuwa har da bidiyoyin soyayyarsu da Kano state material din.
Yanzu haka dai Sadiya bata gidan Al’amin inda a kwanaki kotu da bayar da umarnin cewar G Fresh zai iya zuwa bikon matarsa kamar yada addini ya tanadar tunda dai bai saketa ba har yanzu.