Dakta Hadiza Balarabe
Hadiza Sabuwa Balarabe, ‘yar siyasa ce kuma likita wadda ta kafa tarihi a shekarar 2019, inda ta zama Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna. Har ila yau, ita ce mace ta farko da ta fara zama Maitaimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, sannan inda ta ci gaba da yin wannan aiki bisa sadaukarwarta.
Har wa yau, a matsayinta na kwararriyar likitar; kuma mai ba da shawara sakamakon kwarewar da take da ita a fannin sama da shekaru ashirin, Dakta Hadiza Balarabe; ta bayar da gudummawa sosai wajen inganta harkokin kiwon lafiya a Nijeriya.
Ta fara aiki a shekarar 1990, a babban asibitin Wuse da ke Abuja, inda ta yi aiki a matsayin babbar jami’ar lafiya, daga nan kuma ta yi ayyuka daban-daban a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kafin ta ki ga samun mukamin shugabanci a fannin kiwon lafiya na jama’a, ciki har da daraktar kula da lafiyar jama’a a Babban Birnin Tarayya Abuja.
A shekarar 2019, ta gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, sabon kasafin kudin shekarar 2020 a madadin gwamnan, inda ta zama mace ta farko da ta yi hakan a Arewacin Nijeriya.
Bugu da kari, Dakta Balarabe ta ci gaba da kasancewa mai mutukar himma a cikin shirye-shiryen karfafa al’umma da shawarwari. Sannan, ta kasance mai daidaita al’umma tare da karfafa matasa, domin ci gabansu mai dorewa.
Hajara Adeola
Hajara Adeola kuma, ita ce Shugabar Bankin LOTUS (LOTUS Bank Limited), ta kuma rike matsayin shugaba kuma Darakta a Kamfanin Lotus Capital (Lotus Capital Limited), wani kamfani na Nijeriya; wanda ya shahara da aikinsa na farko a harkar sarrafa kadarorin Shari’a, ayyukan ba da shawarwari na sarrafa dukiya da harkokin kudi.
 Kafin Bankin LOTUS da kuma Kamfanin na Lotus Capital, Adeola ta rike manyan mukamai a manyan cibiyoyin hada-hadar kudi, musamman, inda ta yi aiki a matsayin Daraktar ‘CCT Islamic Finance a UBS Warburg’, inda take kula da asusun kudin Musulunci na Landan. Sannan kuma, ta yi fice a matsayin Manazarciyar Binciken Hadin Kan Muhimmai a BNP Paribas da London.
Adeola ta zama shugaba ta farko, a kungiyar ma’ajiyoyin Nijeriya. Dangane da matsayin da take rike da shi a halin yanzu, Adeola ta shugabanci kwamitin tsare-tsaren babbar kasuwar hannun jari da babu ruwa a cikinsa tsawon shekara 10, kazalika mace ce mai son ci gaba; wajen habaka harkokin kasuwanci.
Bugu da kari, Adeola Darakta ce a Gidauniyar Aliko Dangote, inda ta dukufa sosai ga ayyukan jin kai tare da ci gaban al’umma baki-daya.
Ambasada Fatima Kyari Mohammed
 Ambasada Fatima Kyari Mohammed, Babbar Jami’ar Tarayyar Afirka Mai Sa Ido a Majalisar Dinkin Duniya. Kafin a ba ta wannan mukami, ta kasance babbar mai ba da shawara ta musamman ga Kungiyar Bunkasa Tattalin Arziki ta Yammacin Afirka (ECOWAS), tare da wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin da kuma ci gaban kungiyoyi.
 Ta kuma yi aiki a matsayin Babbar Daraktar Tuntuba kan Tsaro da Sulhu a Afirka ta Yamma ‘Conflict and Security Consulting’. Sannan ta yi aiki a matsayin Manajar Shirye-shirye a Tawagar Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, sannan kuma ta rike mukamin Manajar Ayyuka ta Yanki da Tsaro a Afirka.
 Ambasada Fatima Kyari, ita ce wacce ta kafa wata kungiya mai zaman kanta (LikeMinds), haka zalika; ta sadaukar da kanta wajen taimaka wa al’umma daban-daban musamman masu rauni a Nijeriya. Wannan kungiya da ta kafa, tana karfafa wa mata da matasa guiwa tare da bayar da tallafi ga marayu da yara masu rauni.
 Har ila yau, Ambasada Fatima; ta ba da gudunmawa matuka wajen samar da zaman lafiya. Sannan, an amince da ita a matsayin daya daga cikin mata 100 mafi tasiri cikin matan Afirka ta hanyar yin amfani da kafafen yada labarai (Abance Media) a shekarar 2021 da 2022. Haka zalika, kungiyar ‘NCWG International’ ta zabe ta, ta kuma karrama ta a matsayin macen da take son kawo zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Halima Ibrahim Abba
Halima Ibrahim Abba, kwararriya ce a fannin harkokin kudi; wacce ta shafe sama da shekaru 13 a ciki, sannan kuma shugabar Gidauniyar ‘Skills Outside School Foundation’, wacce ta yi fice a Afirka, kana kuma tana matukar yin kokari wajen samar da aikin yi da kasuwanci, tana kuma bayar da shawarwarin bayanai da na dabaru tare da abokan tarayya da jajircewa a duk fadin Nijeriya da sauran makamantansu.