Wasu gungun ‘yan daba da ake kyautata zaton barayi ne, sun afka Kamfanin jaridar Prime Times News sun yi awon gaba da Kayan aiki masu dimbin yawa.
Lamarin ya faru ne a Ofishin jaridar Dake Kano a ranar Alhamis din da ta gabata, inji jaridar Alkibla.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanan sun balle kofofin Ofishin mai lamba D51 dake rukunin shagunan Al-hamsad Zoo road, inda suka sace kayan aiki da akalla kudin su ya haura miliyan guda.
Daga bisani kuma suka cinna wuta a wurin wanda yayi sanadiyyar asarar Sauran kayayyakin kafin akawo agaji.
An rahoto cewa, kamfanin na jaridar, mallakin Alhaji Ibrahim Garba Shu’aibu ne, take ya bayar da sanarwar dakatar da ayyukan Kamfanin na bangaran bidiyoyi zuwa wasu lokuta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp