Alhaji Aliyu Salihu, mahaifin kakakin majalisar dokokin Jihar Kwara, Injiniya Yakubu Danladi Salihu, ya rasu.
Salihu, mai suna Tafakin Borgu na Masarautar Borgu, ya rasu ne a ranar Juma’a, kuma an binne shi a ranar Asabar a gidansa na kasar Gwanara, a Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara.
- 2023: Muna tattaunawa da Peter Obi kan yiwuwar hada takararmu — Kwankwaso
- Babu Maganar Janye Wa Ahmed Lawan Takara — Hon. Bashir Machina
An sanar da rasuwar malamin wanda tsohon kansila ne a tsohuwar masarautar Borgu, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Salihu Mohammed.
“Tare da godiya ga Allah Madaukakin Sarki, iyalan Alhaji Salihu na sanar da rasuwar mahaifansu kuma babban malami mai suna Alhaji Salihu Aliyu Gwanara, Tafarkin Borgu na Masarautar Borgu. Alhaji Salihu Aliyu tsohon kansila ne a tsohuwar masarautar Borgu,” in ji sanarwar.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Danladi Salihu, ya bayyana rasuwar mahaifinsa a matsayin babban rashi ga iyalansa da al’ummar Gwanara da daukacin al’ummar tsohuwar masarautar Borgu.
Ya ce, marigayin ya yi rayuwa wajen yi wa al’ummarsa hidima tare da yin abubuwan da suka dace ga kowa da kowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp