A yau,filin ya yi muku tsaraba ne tare da waiwaye a don tafiya a kan wasu hakkokin miji da suka kamata mata su rika mayar da hankali a kai tare da saukewa don kara kyautata zamantakewar aure.
Ya kasance matar aure ta zamanto mai mutunta aure saboda zaman gidan miji shi ne rufin asiri da cikar daraja gare ta.
Kula da hakkokin aure ga mace shi ne asirin jin dadin rayuwar aure da zaman lafiya a tsakanin ma’aurata, saboda haka wajibi ne mace ta kula da hakkokin da kanta ko dan ingantuwar zaman aure.
Ga wasu daga ciki kamar haka:
- Akwai Karin Damammaki Ga Zuba Jarin Waje A Kasar Sin
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 A Kasuwa A Zamfara
Ya zamo mace na yi wa miji biyayya sau da kafa cikin abin dabai sabawa dokar Allah ba. Wajibi ne mace ta bi umarnin mijinta ta hanyar aikata abin da ya sa ta da barin abin da ya hana ta cikin girmamawa da nuna yarda.
Kamar yadda za ki yi wa mahaifanki biyayya cikin abin da suka umarce ki, haka ma wajibi ne ki yi wa mijinki biyayya, koma fiye da haka.
Mace tilas ne ta lura da dukiyar mijinta ta hanyar tattalin abinda ya ba ta da kiyaye abubuwan da ya tanada don rayuwar yauda kullum.
Yin almubazzaranci ko wulakanta dukiyar miji na jawo bacin rai ga mai gida,sannan ga tsoron fushin Allah. Mace ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba sai da izinin sa, koda gidan mahaifinta ne. Ta kare kanta daga mazajen da ba nata ba ta hanyar gujewa magana da su komatsanancin kallo da dai sauran abubuwan da ya saba wa shari’a.
Mace ta guji fidda halittarta ko caba ado da turare mai kamshi lokacin da lalura ya sanya za ta fita daga gidanta. Mafi yawan mata ba su tashi ado da sa kaya masu dauke hankali sai za su fita unguwa. Wannan mummunan dabi’a ce da take yada alfasha a bayan kasa.
Mace ta zamo mai tsoron Allah ta yadda za ta kaunaci rahamar Allah a lahira maimakon bin tafarkin bokanci ko sihiri don a mallake miji ko korar kishiya. Zuwa wurin boka tare da gasgata shi masiba ce maitsanani da ke halakar da mai yi.
‘Yan uwa mata ku nisanci bin wannan kazamar hanya mai tabarwa na bin bokaye don gujewa azabar Allah da kwadayin rahamarsa.
Hakuri da biyayya da kyautatawa da soyayya da tsafta da agazawa da sauran dabi’u masu kyau suke kawo zaman lafiya tsakanin ma’aurata ko kishiyoyi ba shaidanin boka ba.
Domin haka ya kamata mata su kula da wadannan abubuwa wajen samun zamantakewar aure mai dorewa a cikin rayuwa. Idan aka rike wadannan abubuwa to za a sami karancin rabuwar aure.
Allah ya sa mu dace.