Wata kungiyar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa karkashin jagorancin ‘yan kasa ‘The Natives’ ta yabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kan yadda ya bayyana a fili cewa zai cire tallafin man fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Kungiyar da ke yaki da zagon kasa, ta yi alkawarin tsayawa kai da kai don ganin Tinubu ya cika wannan alkawarin cikin gaggawa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a lokacin da yake jawabi a wani taron cin abincin rana da ‘yan kasuwa suka shirya masa mai taken, “Business Forward” a ranar Alhamis a Wings, Victoria Island, Legas, ya yi alkawarin cire tallafin man fetur idan aka zabe shi ko da kuwa za a kwashe tsawon watanni ma’aikata na masa zanga-zanga.