Wasu manyan kwamandojin barayin daji a Jihar Katsina, sun miƙa wuya bayan wani sulhu da wata ƙungiya ta yi da su.
Ƙungiyar ta ce wasu daga cikinsu sun ajiye makamansu yayin da wasu suka ce suna riƙe da su ne don kariya daga ɓarayin da ba su yarda da sulhu ba.
- Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
- Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
Kwamared Hamisu Sai’idu Batsari ya ce, “Daga cikin waɗanda suka miƙa wuya akwai Abu Radda da Maikada da Umar Blak da Tukur Dannajeriya.
ADVERTISEMENT
“Abu Radda yana da fiye da yara 500 a ƙarƙashinsa.”
Ya kuma ƙara da cewa, “Ƴan bindigan sun buƙaci gwamnati ta daina kama su ba tare da laifi ba, kuma idan sun yi laifi, a gurfanar da su a kotu kamar yadda doka ta tanada.”














