Wasu da ba a san ko suwaye ba, sun yi wa malami a Sashen Nazarin Jiki da Lafiya na Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), Dr. Kamar Abdulkadir, kisan gilla a ofishinsa.
An kashe Abdulkadir ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da maharan suka kutsa cikin ofishinsa suka kai masa hari da wuka da guduma.
- Tinubu Zai Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Senegal
- An Dakatar Da Shugabar Matan APC A Kaduna Kan Sukar Uba Sani
Majiyoyin leken asiri sun bayyana wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa, an ga gawar mamacin a cikin jini tare da rauni da dama a jikinsa daga hannun wadanda suka kashe shi.
Maharan sun kuma tafi da motarsa da wasu kayayyaki masu daraja, amma an bayyana cewa, hukumomi na neman wadanda suka aikata wannan mummunan lamarin.
Rundunar ‘yansandan jihar Borno ta bayyana cewa, ta cafke mutane 8 da take zargi kan aikata wannan mummunan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp