Sojoji da dama sun shiga hannu, ciki har da jami’an kabilar Zaghawa na shugaban kasar Chadi, Janar Mahamat Idris Deby a karshen mako kan zargin kitsa juyin mulki a kasar.
Rahotanni sun ce yanzu haka ana tsare da su zuwa lokacin da jami’an hukumar leken asirin kasar za su kammala bincike. Rahoton BBC Hausa.Â
Babu wata sanarwa a hukumance daga mahukuntan kasar a kan zargin kitsa juyin mulki, amma bayanan hakan sun fito ne bayan da aka murkushe wasu ‘yan adawa a wata gwabzawa da aka yi tsakanin jami’an sojin da kuma ‘yan adawa a watan Oktoban da ya gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp