Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano da Jigawa da Katsina (KEDCO) ya katse wutan lantarki ga Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, saboda basussukan da ake binta da ya kai har Naira miliyan ₦248m.
Alhaji Abubakar Yusuf, Manajan Daraktan KEDCO ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, a yau Litinin, Naira miliyan ₦20m ne kacal jami’ar ta iya biya a cikin bashin.
- NLC Na Gudanar Da Zanga-zanga A Ofishin KEDCO Na Kano Kan Ƙarin Ƙuɗin Wutar Lantarki
- Za A Yi Sallah Babu Lantarki A Jahohin Kano, Jigawa, Katsina, Ma’aikatan KEDCO Sun Shiga Yajin Aiki
Yusuf ya bayyana cewa KEDCO ba ta da wata mafita illa ɗaukar wannan tsattsauran mataki, inda ya jaddada mahimmancin jami’ar na biya kuɗin da ya kamata kafin a dawo da wutar lantarki.
Ya nanata matsayin kamfanin na cewa ba tare da biyan kudi ba, jami’ar za ta ci gaba da zama cikin duhu.