Alkalin wata babbar kotun tarayya karkashin mai shari’a Liman, ta bayar da umarnin hana gwamnatin jihar Kano mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II. An bayar da umarnin ne a daren ranar Alhamis, duk da cewa a halin yanzu alkalin yana Amurka. Aminu Babba-Dan’Agundi, mai rike da sarautar Sarkin Dawaki ne ya shigar da karar.
Kotun ta yi amfani da wannan shigar da karar wajen bayar da izini ga Sarkin Dawaki da ya gabatar da duk sauran hukunce-hukuncen kotu, kuma an umurci duk ɓangarorin biyu mai kara da wanda ake kara da su jira har zuwa lokacin sauraron karara ranar 3 ga Yunin shekarar da muke ciki.
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamna Yusuf Ya Mayar Da Sanusi II A Matsayin Sarkin Kano
- Gwamantin Kano Ta Hana Tsohon Sarki Aminu Ado Dawo Wa Jihar Kano
Domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar, kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da wadanda ake kara aiwatar da sabuwar dokar Majalisar Dokokin Masarautar Kano. Alkalin kotun ya jaddada cewa ya kamata bangarorin su ci gaba da bin doka da kuma amincewa da kudirin har sai an saurari bukatar mai kara saboda mutunta yancin dan Adam na kai kara kuma a saurare shi.
Kotun dai ta dage sauraren karar ne zuwa ranar 3 ga watan Yuni na 2024.