Gwamanti jihar Kano ta dakatar da yunƙurin da tsohon sarki Aminu Ado Bayero ya yi na dawo wa jihar domin ya kwashi kayansa zuwa kwanaki wa’adin sa’o’i 48 da gwamnatin ta gindaya wa duk sarakunan da aka tsige.
Rahotanni sun bayyana cewa, Aminu Ado ya je garin Ijebu-Ode, da ke jihar Ogun domin ganin Oba Sikiru Adetona, na Masarautar Ijebu domin neman shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya dakatar da yunƙurin tsige shi.
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamna Yusuf Ya Mayar Da Sanusi II A Matsayin Sarkin Kano
- Xi Ya Yi Kira Da A Kara Zurfafa Sauye Sauye Masu Nasaba Da Zamanantarwa Irin Ta Sin
Sai dai wani rahoto da jaridar Daily Nigerian ta buga, ya tabbatar da cewa, gwamnatin jihar Kano ta samu labarin yunƙurin tsohon sarkin na dawo wa Kano, nan da nan, ta sanar da jami’an tsaro domin su hana shi shigo wa jihar domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Wata majiya ta tabbatar da cewa, an hangi motocin fadar sarki a filin jirgin saman Kano suna tsumayin dawowar tsohon sarkin amma daga baya aka umarce su da su koma Fada.
Da safiyar yau ne jaridar LEADERSHIP HAUSA ta kawo muku rahoton cewa majalisar dokokin jihar Kano ta rushe dokar da ta kafa Masarautun Kano guda biyar da suka haɗa da Kano da Bichi da Rano da Karaye da Gaya da aka yi a shekara ta 2019 kuma gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu.
Tuni gwamnan ya bayyana sunan Muhammadu Sanusi II a matsayin wanda zai dawo masarautar ta Kano.