’Yansanda a Akure, Jigar Ondo, sun kama wata mata da ake zargi da kashe ’yar uwarta kan bashin Naira 800.
Matar da ake zargi mai suna Bosede Iluyemi, ’yar kasuwa ce.
- Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
Ta nemi ’yar uwarta, Omowumi Tewogboye, ta biya kuɗin tumatir da barkono da ta karɓa bashi a wajenta.
Rigima ta tashi a tsakaninsu, inda Bosede ta ta kama Omowumi da rigima.
Omowumi ta faɗi ƙasa, inda ta ji mummunan rauni.
An garzaya da ita asibiti, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
’Yansanda sun kama Bosede kuma suna bincike a kan lamarin.
Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya ce za su tabbatar da adalci.