An kama wata mace mai suna, Ifeoma Ossai, saboda zargin kashe mai gidan da take haya a garin Surulere Oladele na jihar Ogun.
‘Yansanda sun kama Ossai ne sakamakon rahoton da suka samu daga Olaleye Taiwo.
- An Fitar Da Tsarin Yin Kwaskwarima Na JKS Da Hukumomin Gwamnati
- Dan Majalisar Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fita Yakin Neman Zabe A Bauchi
Wanda ya yi karar, ya gaya wa ‘yansanda cewa, bayan dan uwansa mai suna Oladele sun samu sabani da mai haya a gidansa kan biyan kudin wuta wanda har ta kai ga yin fada a lokacin da ake fafata wa ne, ‘yar hayar caraf ta kame mazakutar mai gidan nasu ta murde.
Kamar yadda mai magana da yawun rundunar ‘yansanda na jihar Ogun, ya bayyana na take mai gidan ya fadi sumammae, daga nan a ka dauke shi zuwa asibitin Ota, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Samun wannan labara ke da wuya, sai DPO na Ota CSP Saleh Dahiru, tare da jama’arsa suka tafi inda wannan abin ya faru, inda kuma suka samu nasarar kama wadda ake zargin.
Lokacin da ake yi mata tambayo, wadda ake zargi da yin kisan kan ta ce “Wanda aka kashen ya tambayeta ta biya kudin wuta, a kan haka suka fara ka-ce-na-ce,abu kamar wasa ya rikide ya zama fadal.
Bayan sun kaure da kokawa, sai kawai ta yi caraf, ta kama mazakutarsa ta mured, nan take ya fadi kasa.
Oyeyemi ya ce, yanzu haka gawar mutumin na asibiti, inda za ayi bincike.
Sannan kuma kwamishinan ‘yansanda Frank Mba, a kai wadda ake zargin sashin binciken wadanda ake zargi da laifin kisan kai, domin yin cikakken bincike.