Wata yarinya ‘yar shekara hudu a Kano ta rasu bayan ta faɗa rijiya a unguwar Kofar Waika da ke cikin jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwana-kwana na Jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya fitar da sanarwar, inda ya bayyana faruwar lamarin da tsakar ranar Litinin.
Saminu, ya ce an sanar da su faruwar lamarin da misalin karfe 02:05 na rana, kuma nan-take suka hanzarta zuwa ceto yarinyar, sai dai a lokacin da aka dauko yarinyar tuni ta riga ta rasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp