Kawo yanzu dai dan wasa Marcus Rashford, dan kwallon tawagar Ingila, Marcus Rashford wanda ba ya kan ganiya, yana fuskantar kalubale a Manchester United a kakar bana.
Dan wasan mai shekara 26 ya kasa ci gaba da nuna irin kwazon da ya yi a bara, inda ya ci kwallo 30 a dukkan fafatawa a kungiyar kuma Rashford ya taimaka wa United ta dauki Carabao Cup da samun gurbin Champions League a kakar da ta wuce.
- Minista Idris Ya Ƙaddamar Da Ƙungiyar Kakakin Labarai
- AFCON 2023: Masu Masaukin Baƙi Sun Fitar Da Ƙasar Mali
A kakar wasa ta shekara ta 2023 zuwa 2024, ya ci kwallo hudu a wasanni 26 da ya buga wa Manchester United – kenan kwazonsa ya yi kasa sosai, musamman a Premier League.
Saboda haka wasu ke cewa ya kamata Erik ten Hag ya sayar da Rashford ko kungiyar za ta samu kudin sayen wani dan kwallon domin ta kara karfi. To sai dai kuma ba matsalar Rashford kadai United, wadda aka fitar daga Champions League da Carabao Cup da ta dauka a bara ke fustanta ba a kakar nan.
Kungiyar wadda take ta takwas a kan teburin Premier League da maki 32 bayan wasa 21 ta kai zagaye na biyar a FA Cup bayan ta doke kungiyar Newton County a ranar Lahadin da ta gabata.
A bara ne Rashford ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Manchester United zuwa karshen kakar wasa ta 2028 kan £325,000 a duk mako sannan tun farkon kwantiragin dan kwallon tawagar Ingila zai kare ne a karshen kakar shekara ta 2023 zuwa 2024.
Dan wasan ya taka rawar gani a bara karkashin Erik tten Hag da cin kwallo 30 a wasa 56 a dukkan fafatawa domin ya fara buga wa United wasa a shekarar 2016 a wasa da Midtjylland, kuma kungiyoyi da yawa sun so daukar Rashford a kakar da ta wuce, bayan rawar da ya taka.
Rashford na daya daga cikin ‘yan kwallon Ingila da suka fuskanci kalaman wariya, bayan da ya barar da fenariti a wasan karshe da Italiya a Euro 2020, sannan cikin Agustan shekara ta 2021 ya ji rauni a allon kafada a kakar da ya ci kwallo biyar da ta kai an sallami Ole Gunnar Solskjaer aka maye gurbinsa da Ralf Rangnick.
Bugu da kari, kociyan tawagar Ingila, Gareth Southgate ya ajiye Rashford daga buga wasa hudu a Nations League a cikin watan Yunin shekara ta 2022 sakamakon rashin tabuka abin kirki.