Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano.
Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025.
- Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5
- Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin Jihar
Nadin Na Ibrahim zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Febarairun 2025.
Sanarwar nadin ta bayyana cewa an zabi, Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar saboda shafe sama da shekaru talatin ya na aikin gwamnati da tarin kwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na gwamnati da ya yi aiki, don cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da jihar Kano gaba.
Nadin na Umar Farouk Ibrahim, na zuwa ne watanni biyu bayan sauke tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Dr. Baffa Abdullahi Bichi daga muƙaminsa a sakamakon dalilan rashin lafiya, kamar yadda sanarwar sauke shi ta bayyana haka a baya. Sai dai duk da haka wasu na ganin kamar akwai wasu dalilai na siyasa saɓanin wanda aka bayyana na sauke Baffa Bichin.