Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa sakataren zartarwa na hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA), Injiniya Shehu Ahmed Hadi, wa’adin sa’o’i 24 da ya bayyana matsayin gwamnati dangane da rushe wank bangare na babban masallacin kasa da kuma tsarin biyan diyya.
Wasu sassan filin masallacin na kasa za su fuskanci rusau sakamakon aikin fadada hanyoyi, lamarin da ya sa mahukuntan hukumar ke neman a biya su diyya.
- Tabbatar Da Daidaito Da Cin Moriyar Juna Suna Cikin Babban Ruhin Shawarar BRI
- Mutum 38 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe
Ministan ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na babban Masallacin kasa da ke Abuja karkashin jagorancin shugaban kungiyar Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar.
Sai dai ya kuma karyata rahotannin da ke cewa ministan na shirin yaki da addini ne.
Wike ya soki wadanda ke shirin fakewa da addini domim cimma wani mugum nufinsu.
Wike ya lura cewa a matsayinsa na dan Nijeriya, ba shi da wani dalili na furta kalaman kyama ga wata kungiyar addini, sai dai ya goyi bayan duk wanda ke da manufa ta gaskiya.
A yayin da yake ba da tabbacin cewa FCTA ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafawa kula da Masallacin kasa da kuma Cibiyar Kula da Lafiyar Jama’a ta kasa, Wike ya yi kira ga malaman addini da su yi kira don samun hadin kai da zaman lafiya.
Tun da farko Etsu Nupe ya bukaci ministan da ya ba da goyon bayan aikin kula da masallacin, wanda ya ce an dade ana yi ba tare da an kammala ba.
Ya kuma roki ministan da ya kara bai wa kwamitin lokaci domin bunkasa filayen da FCTA ta ware masa.